Najeriya

Buhari na shirye-shiryen cafke ni - Obasanjo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo. AFP

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da shirye-shiryen kama shi akan zarge-zargen karya domin haramta mishi fadin albarkacin bakinsa.

Talla

Sanarwar da shugaban ya fitar ta hannun kakakinsa, Kehinde Akinyemi, ta zargi Buhari da yunkurin yin amfani da takardu, da kuma shaidun karya wajen tuhumarsa.

Obasanjo ya ce daga cikin hanyoyin da gwamnatin Buhari ke shirin amfani da su, wajen rufe masa baki, akwai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, wadda ke shirin bincikar gwamnatinsa da ta shude, ta hanyar amfani da shaidun na karya, hadi da takardun boge.

Tsohon shugaban ya ce majiyoyin da ke kusa da gwamnatin shun shaida masa cewa, an sanya shi cikin mutanen da ake sa ido akansu, kuma babu wanda yake da tabbacin makomarsa.

Obasanjo ya ce wannan mataki zai mayar da gwamnatin Najeriya, kamar ta zamanin Sani Abacha, yayin da ya ce babu wani mataki da zai sa shi  rufe bakinsa, ko kuma razana shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.