Najeriya

Gwamnati ta maida wa Obasanjo martani kan zargin shirin kama shi

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. AFP / Seyllou

Gwamnatin Najeriya ta mai da martani kan zargin da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya yin a cewa shugaba Buhari yana shirye-shiryen kama shi, ta hanyar amfani da zarge-zarge hadi da shaidun karya.

Talla

Tsohon shugaban ya bayyana zargin ne a ranar Juma’a, inda yace yunkuri ne kawai na hana shi fadin albarkacin bakinsa.

Kan haka ne ministan yada labaran Najeriya da raya al’adu, Lai Muhd ya ce gwamnatinsu ba za ta taba bata lokacinta wajen yi wa wadanda basu aikata laifi kage ba, domin abinda ta sa a gaba shi ne gayarn barnar da gwamnatocin baya suka tafka tsawon shekaru 16.

A cewar Ministan yada labaran, yayinda hankulan masu gaskiya ke kasancewa a kwance, marasa gaskiyar kuwa ko a ruwa gumi suke yi.

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ta hannun kakakinsa Kehinde Akinyemi ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da shirye-shiryen kama shi akan zarge-zargen karya domin haramta mishi fadin albarkacin bakinsa.

Obasanjo ya ce daga cikin hanyoyin da gwamnatin Buhari ke shirin amfani da su, wajen rufe masa baki, akwai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, wadda ke shirin bincikar gwamnatinsa da ta shude, ta hanyar amfani da shaidun na karya, hadi da takardun boge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.