'Yan kunar bakin wake sun hallaka mutane da dama a Damboa

Wasu jami'an agaji yayin bai wa wadanda hare-haren kunar bakin wake suka rutsa da su taimako a Damboa, Jihar Borno.
Wasu jami'an agaji yayin bai wa wadanda hare-haren kunar bakin wake suka rutsa da su taimako a Damboa, Jihar Borno. AFP/Getty Images

Rahotanni sun akalla mutane 31 ne suka hallaka, wasu 48 kuma suka jikkata a wasu hare-haren kunar bakin wake da mayakan Boko Haram suka kai kan jama’a a Shuwari da Abachari da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno.

Talla

Wasu shaidun gani da ido da suka hada da, mazauna kauyen da kuma jami’an kato da gora, sun ce ‘yan kunar bakin waken su shida, sun kai harin ne kan jama’a, yayin murnar ranar Sallah a ranar Asabar.

To sai dai a wani yanayi na samun bayanai masu cin karo da juna, rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce mutane 20 ne suka hallaka sakamakon hare-haren kunar bakin waken, wasu 48 suka jikkata, sabanin yawan mutane 31 da wasu mazauna unguwar ke ikirarin sun rasa rayukansu.

Wakilinmu a Maiduguri, Bilyaminu Yusuf ya aiko mana da rahoto a kan harin.

'Yan kunar bakin wake sun hallaka mutane da dama a Damboa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.