Wasanni-Najeriya

Super Eagles ta Najeriya ta lallasa Iceland da ci 2 da nema

Yanzu haka dai Najeriyar na da maki 3 yayinda jagaba a rukunin Croatia ke da maki 6 sai kuma Iceland da Argentina wadanda ke da maki daddai.
Yanzu haka dai Najeriyar na da maki 3 yayinda jagaba a rukunin Croatia ke da maki 6 sai kuma Iceland da Argentina wadanda ke da maki daddai. REUTERS/Jorge Silva

Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu da nema a wasannin zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Rasha. Yanzu haka dai Najeriyar ita ke matsayin ta biyu a a yawan maki rukuninsu na D.

Talla

Tun farko dai Najeriyar ta sha kaye a hannun Croatia da ci 2 da nema a sabar din makon jiya zagayen farko kenan na gasar cin kofin duniyar, matakin da ya sa ta zama koma baya a jeerin kasashe 4 na rukunin D.

Sai dai nasarar Najeriyar ta yau da ci biyu da nema ta hannun dan wasanta Ahmad Musa a minti na 49 da kuma na 75 ya bata damar zama ta biyu a jerin kasashen hudu na rukunin D.

Yanzu haka dai Najeriyar na da maki 3 yayinda jagaba a rukunin Croatia ke da maki 6 sai kuma Iceland da Argentina wadanda ke da maki daddai.

Nasarar ta Najeriya dai ta zo a bazata ganin yadda da dama daga al'ummar kasar ke ganin kadan ya rage mata ta tattaro kayanta ta koma gida, la'akari da rashin tabuka abin kirki a wasan zagayen farko, ko da dai wasu na dora laifin kan Kociyan tawagar Gernot Rohr wanda ya musanya wuraren da wasu 'yan wasan ke taka leda.

Sai dai a wasan na yau Rohr ya sauya wasu daga cikin guraben da 'yan wasan suka taka leda a farko, inda ya mayar da su guraben da suka fi kwarewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI