Bakonmu a Yau

Marie Saragosse kan ziyarar sashen hausa na RFI

Sauti 04:15
Shugabar rukunin gidajen yada labarai na Faransa, Marie Christine Saragosse
Shugabar rukunin gidajen yada labarai na Faransa, Marie Christine Saragosse RFI hausa

Shugabar Kafafen Yada Labaran Faransa da ke yada shirye-shiryensu zuwa kasashen ketare, Marie Christine Saragosse wadda ke tare da wani bangare na tawagar shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke ziyarar aikin yinin biyu a Najeriya daga yau Talata, ta ziyarci ofishin sashen hausa na RFI da ke birnin Legas. Saragosse, ta bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal wasu daga cikin dalilan da suka sa ta ziyarci tashar RFI Hausa, tare da sanar da wasu daga cikin sauye-sauyen da take kan aiwatarwa a kafafen yada labaran da take jagoranta.