Najeriya

Kotun kolin Najeriya ta kawo karshen shari'ar Saraki

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki. REUTERS/Afolabi Sotunde

Kotun kolim Najeriya ta wanke shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa na saba ka’idar aiki, ta hanyar boye bayanan wasu kadarori da ya mallaka.

Talla

Alkalan kotun kolin biyar da ke sauraron daukaka karar Saraki karkashin jagorancin mai shari’a Dattijo Muhammad sun amince da soke shar’ar wadda da fari aka shigar da ita gaban kotun da’ar ma’aikata.

Yayin yanke hukuncin, majalisar alkalan kotun kolin sun ce hukuncin soke shari’ar ya biyo bayan, rashin tabbatacciyar shaida daga lauyoyi masu shigar da kara.

A watan Yulin shekarar 2017, kotun da’ar ma’aikata a karkashin mai shari’a Danladi Umar,ta kawo karshen karar da lauyoyin gwamnati suka shigar gabanta na zargin shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki da aikata laifuka 18, da suka shafi saba ka’idar aiki. Daga bisani kotun ta yi watsi da baki dayan zarge-zargen da ake yi wa Saraki, saboda rashin kwararan hujjoji.

Sai dai biyo bayan garzayawa zuwa kotun daukaka kara da gwamnatin Najeriya ta yi, a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2017, kotun ta yanke hukuncin maido da tuhume-tuhume 3 daga cikin 18 da gwamnatin ke yi wa shugaban majalisar dattijan, zalika kotun daukaka karar ta bai wa Saraki umarnin ya koma gaban kotun da’ar ma’aikatan don kare kansa.

Hukuncin kotun daukaka karar ne ya sanya dukkanin bangarorin gwamnati da kuma Bukola Saraki suka rankaya kotun koli inda shugaban majalisar dattijan ya nemi kotun ta soke tuhume-tuhume 3 da aka maido kansa, yayinda ita kuma gwamnatin Najeriya ke neman kotun kolin ta maido da sauran tuhume-tuhume 15 da kotun daukaka kara ta soke a baya.

Sai dai yau Juma’a, 6 ga watan Yuli na shekarar 2018, kotun kolin Najeriyar ta yi watsi da bukatar gwamnatin kasar, kana amsa bukatar Saraki, inda ta tabbatar da soke dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa, bisa rashin kwararan hujjoji na shadu daga lauyoyin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.