Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatina na cika alkawuran da ta dauka- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari  da wasu jami'an gwamnatinsa a wurin kaddamar da aikin jirgin kasa na fasinja mai zirga-zirga a Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari da wasu jami'an gwamnatinsa a wurin kaddamar da aikin jirgin kasa na fasinja mai zirga-zirga a Abuja RFI/Kabir Yusuf
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, gwamnatinsa na cika alkawuran da ta yi wa al’ummar kasar, musamman idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ta samu tun bayan kafuwarta.

Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka a yayin kaddamar da kashin farko na aikin jirgin kasan fasinja mai jigila a Abuja wato ARMTP wanda ya laukme kimanin Dala miliyan 823.5.

Buhari ya ce, kaddamar da wannan aiki, na daya daga cikin hujjojin da ke nuna cewa gwamnatinsa na cika alkawuran da ta dauka.

A cewar shugaban, gwamnatinsa ta yi bajinta a bangarorin ilimi da kuma samar da kayayyakin more rayuwa ga al’ummar kasar.

Shugaban ya bayyana kwarin guiwar cewa, wannan aikin da ya kaddamar a ranar Alhamis zai taka muhuimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin birnin tarayya Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.