Najeriya

'Yan takara 34 na fafatawa a zaben Gwamnan jihar Eikiti

An soma zaben gwamnan jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya.
An soma zaben gwamnan jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya. Reuters

A yau Asabar, 14 ga watan Yuli na shekarar 2018, ake zaben Gwamnan jihar Ekiti, wanda ‘yan takara 34 zasu fafata domin darewa kujerar gwamnan jihar.

Talla

Kafin zaben dai alkalaumman hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta sun nuna cewa yawan masu kada kuri’ar da ta yi wa rijista ya kai, dubu 913 da 334, sai dai an tantance dubu 667 da 270 ne daga cikinsu, wato kashi 73 na wadanda suka cancanci kada kuri’ar.

Daga cikin ‘yan takarar da ke neman mukamin gwamnan akawai Kayode Fayemi dan takarar Jam’iyya mai mulki da APC da kuma Kolapo Olusola dan takarar jami’yyar adawa ta PDP.

Sama da jami’an tsaro dubu 30, tare jirage masu saukar ungulu 2, da kuma motocin sintiri 250 aka girke a jihar ta Ekiti domin samar da tsaro yayin zaben kujerar gwamnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.