Najeriya

Ba zan gudu daga Najeriya saboda EFCC ba- Fayose

Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele Fayose.
Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele Fayose. Pulse.ng/Twitter/@OfficialPDPNig

Gwamnan Jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele Fayose ya ce, ba zai gudu daga Najeriya ba da zaran wa'adin rigar kariyarsa ya kare a cikn watan Oktoba mai zuwa, yayin da rahotanni ke cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC ta yi barazanar gudanar da bincike a kansa da zaran ya kammala wa'adinsa.

Talla

Mai magana da yawun Fayose, Lere Olayinka ya shaida wa manema labarai cewa, babu abin da gwamnan ke tsoron sa, in da ya ce, “me za a yi ma shi? Shin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC ita ce kotun shari'a?”.

A cewar Lere ya gana da gwamnan game da makomarsa ba tare da rigar kariya ba bayan karewar wa’adinsa na gwamnan Ekiti.

A ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa ne ake saran Fayose na jam’iyyar adawa ta PDP ya mika mulki ga Kayode Fayemi da ya lashe zaben gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC a ranar Asabar da ta gabata.

Mr. Fayemi ya lashe zaben ne bayan ya yi nasarar doke mataimakin gwamna a EKiti kuma dan takarar PDP, Kolapo Olusola-Eleka.

Jim kadan da ayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi, aka fara rade-radin cewa, akwai yiwuwar Fayose ya tsere daga Najeriya don kauce wa gurfana a gaban shari’a da zaran ya mika mulki nan da watanni uku masu zuwa.

Hukumar EFCC ta yi barazanar bincikar Fayose kan zarge-zargen almundahana a wani aikin kiwon kaji a shekarar 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.