Bakonmu a Yau

Chief Sylvanus Lot kan tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya a jihar Filato

Sauti 04:37
Wasu Fulani makiyaya a Tarayyar Najeriya.
Wasu Fulani makiyaya a Tarayyar Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Wasu dattawan Jihar Filato da ke Najeriya sun bayyana damuwar su kan tashe tashen hankalun da ake cigaba da samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Yankin Arewacin Jihar, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar da su hada kai domin shawo kan sa.Dattawan sun kuma yi Allah wadai da yadda wasu matasa suka kai hari kan tawagar gwamna da gidan gwamnati, da kuma yadda ake tare mutane akan hanya ana kashewa da zarar an samu matsala a kauyuka, inda suke danganta matsalar da siyasa.Mai Magana da yawun dattawan, kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar a karkashin gwamnatin Sir Fidelis Tapgun, wato Chief Sylvanus Lot yayi mana tsokaci akai.