Bakonmu a Yau

Haj. Naja'atu kan hukumar 'yan sandan Najeriya

Sauti 03:24
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya REUTERS/Austin Ekeinde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda, in da ya umurce su da su tabbatar da inganta ayyukan rundunar da kuma dawo ma ta da kimarta. Hukumar za ta yi aiki ne a karkashin tsohon Sufeto Janar Musiliu Smith. Akan wannan ne Kabir Yusuf ya tattauna da Hajiya Naja’atu Muhammad, daya daga cikin Kwamishinonin hukumar.