Kotun Amurka ta yi watsi da bukatar kungiyar IPOB kan Najeriya

Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar IPOB a birnin Aba. 28 ga watan Mayu, 2017.
Wasu daga cikin magoya bayan kungiyar IPOB a birnin Aba. 28 ga watan Mayu, 2017. STEFAN HEUNIS / AFP

Wata Kotu dake birnin Washington a Kasar Amurka ta yi watsi da karar da Kungiyar dake fafutukar kafa Kasar Biafra ta kai cewa Gwamnatin Najeriya ta ba su Miliyoyin daloli a matsayin diya.

Talla

Kungiyar ta bakin Godson M. Naka sun nemi a basu kashi 40 cikin kudi dala miliyan 550, daga cikin kudaden da aka gano na Abacha a kasashen ketare.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, daya daga cikin ‘yan kabilar ta Igbo, Mazi Obinna Oparumo, ya ce zasu mutunta hukuncin kotun.

Obinna Oparumo kan Kotun Amurka ta yi watsi da bukatar kungiyar IPOB kan Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.