Najeriya

Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi murabus

Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar.
Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar. Naij.com
Talla

Farfesa Hafiz Abubakar ya sanar da matakin nasa ne a wani sakon murya mai tsawon mintuna biyu da rabi, da ya fitar, tare da wata wasika da ya rubuta ga gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar Asabar, 4 ga watan Agusta, 2018.

Yayin sanar da sauka daga mukamin nasa, Farfesa Hafiz, ya ce zai so ya ci gaba da rike nauyin da aka dora masa amma hakan ba zai yiwu ba, lakari da rashin samun daidaito tsakaninsa da gwamnan Kano, kan wasu batutuwa da suka shafi, tsarin tafiyar da gwamnati, siyasa da wasu al’amura da dama.

A cewar tsohon mataimakin gwamnan yayi iyaka kokarinsa wajen jan hankalin Dr Ganduje kan magance banbancin da ke tsakaninsu amma hakan ya faskara.

A makon da ya gabata, Farfesa Hafiz Abubakar ya aike da wasika zuwa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, inda ya ke bayyana cewa akwai wadanda ke barazana ga rayuwarsa.

Murabus din da mataimakin gwamnan ya yi ya zo ne dai dai lokacin da ake zargin, wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jiharsa ta Kano na shirye-shiryen tsige shi, kuma har wasu 31 sun rattaba hannu kan amincewa da daukar matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI