Bakonmu a Yau

Attahiru Bafarawa kan takarar shugabancin Najeriya

Sauti 03:55
Tsohon gwamnan jihar Sokkoto, Attahiru Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sokkoto, Attahiru Bafarawa Bioreports

Yayin da ya rage watanni a gudanar da zaben Najeriya, yanzu haka ' yan takarar neman shugabancin kasar na ci gaba da fitowa suna bayyana aniyarsu a jam’iyyu daban daban. A karshen mako, tsohon gwamnan jihar Sokkoto, Alhaji Attahiru Bafawara, wanda ke cikin 'yan takaran shugabancin kasar a Jam’iyyar PDP, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta kuma bayan dawowarsa jihar Lagos, Bashir Ibrahim Idris ya tambaye shi dalilin ziyarar a dai dai wannan lokaci da gangar siyasa ke kadawa a kasar.