Izang kan dokar cin gashin kan majalisun dokoki
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sauti 03:41
Shugabannin Majalisun Dokokin Najeriya 36 sun gudanar da wani taro a birnin Legas domin tattaunawa kan dokar 'yancin cin gashin kan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu don bai wa majalisun dokokin jihohin 'yancin cin gashin kai ba tare da dogaro da bangaren zartaswa ba, amma sai dai aiwatar da dokar a wasu jihohin ta gamu da cikas. Bayan kammala taron, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato, Rt. Hon Joshua Izang Madaki.