Najeriya

APC ta lashe zaben cike gurbin majalisar dattijai a Katsina

Dan takarar jam'iyyar APC a zaben cike gurbin majalisar dattijai mai wakiltar jihar Katsina, Ahmad Babba-Kaita.
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben cike gurbin majalisar dattijai mai wakiltar jihar Katsina, Ahmad Babba-Kaita. News Agency of Nigeria (NAN)

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya sun ce dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC, Ahmad Babba-Keita, ya lashe zaben cike gurbi na kujerar majalisar dattawa da ya gudana a jiya Asabar.

Talla

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa, Ahmad Babba kaieta wanda a baya dan majalisar wakilan Najeriya ne, ya samu kuri’u dubu 224, 607, inda ya samu nasara akan abokan hamayyarsa biyar.

Dan takara na biyu shi ne Kabir Babba-Kaita a karkashin jam’iyyar PDP,  samu kuri’u dubu 59, 724.

Sauran jam’iyyun da suka fafata a zaben sun hada da GPN da ta samu kuri’u 1056, sai DA mai kuri’u 796, sai kuma MPN mai kuri’u 633 yayinda jam’iyyar MMn ta samu kuri’u 343.

Zaben cike gurbin dai ya biyo bayan rasuwar Sanata Mustafa Bukar a watan Afrilun da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI