Najeriya

PDP na zargin APC da yunkurin kama Saraki

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki, tare da mataimakinsa Ike Ekweremadu.
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki, tare da mataimakinsa Ike Ekweremadu. Daily Post

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana bankado wata makarkashiya da ta ce, jam’iyyar APC mai mulki da fadar shugaban kasa na shiryawa, ta kama shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

Talla

A cewar jam’iyyar ta PDP, gwamnatin APC na shirin amfani da jami’an tsaron kasar da kuma hukumar EFCC mai yakar cin hanci da rashawa wajen gayyatar Saraki da Ekweremadu, daga bisani kuma a tsare su.

Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun kakakinta Mista Kola Ologbondiyan a ranar Lahadi a garin Abuja, PDP ta kuma yi zargin cewa, bukatar da gwamnati ta mika wa ‘yan majalisun kasar da su yi zama na musamman kan kasafin kudin hukumar zabe mai zaman kanta, yana tattare da wata boyayyar manufa.

Zargin na jam’iyyar PDP ya zo ne bayan da a makon da ya gabata, datse kofar shiga zauren majalisun Najeriya da jami’an tsaron farin kaya na DSS suka yi, ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar, lamarin da ya kai ga mukkadashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo korar shugaban hukumar Lawal Daura.

Takaddama na dada yin karfi tsakanin manyan jam’iyyun Najeriya biyu, tun bayan da wasu ‘yan majalisun kasar suka fice daga APC zuwa PDP, ciki har da shugaban Majalisar Dattijan kasar Bukola Saraki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI