Bakonmu a Yau

Isa Sanusi kakakin kungiyar Amnesty kan tsare dan jarida a tarayyar Najeriya

Sauti 02:59
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya.
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya. Reuters

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta bi sahun kungiyar ‘Yan Jaridun Najeriya, da kuma kungiyoyin fararen hula wajen kira ga rundunar ‘Yan Sandan kasar da ta saki Samuel Ogundipe, dan jaridar Premium Times da ta tsare don tilasta masa bayyana sunan wanda ya bashi bayani kan rahotan binciken da Sufeto Janar Ibrahim Idris ya rubutawa mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo kan Lawal Daura.Bisa ka’idar aikin Jarida dai, dan Jarida baya bayyana wanda ya bashi bayanai duk yadda za’ayi da shi.Saboda haka mun tattauna da kakakin kungiyar ta Amnesty Isa Sanusi kan sanarwar tasu, kuma ga bayanin da yayi mana.