Najeriya

Gwamnatin Najeriya na bincike kan muryar Leah Sharibu

Leah Sharibu, daliba daya tilo da Boko Haram ke ci gaba da tsarewa bayan sakin 'yan uwanta dalibai
Leah Sharibu, daliba daya tilo da Boko Haram ke ci gaba da tsarewa bayan sakin 'yan uwanta dalibai soundplus.com.ng

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce tana dakon sakamakon nazarin da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ke yi kan wani sakon murya na Leah Sharibu, dalibar makarantar Dapchi da mayakan Boko Haram ke ci gaba da tsarewa bayan sun saki sauran ‘yan uwanta dalibai mata da suka sace a jihar Yobe.

Talla

A cikin sakon muryar an jiyo Leah na kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaka mata wajen ceto ta daga kangin da ta tsinci kanta a ciki.

Mai Magana da yawun fadar shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce jami’an Tsaron Farin Kayan na nazari kan muryar wadda jaridar 'The Cable' ta wallafa a shafin itanet a ranar Litinin, yayin da ya ce gwamnati za ta mayar da martani bayan kammala binciken.

A ranar 19 ga watan Fabairun daya gabata ne, mayakan Boko Haram suka far wa makarantar sakandaren Dapchi tare da sace dalibai mata 110 da suka sako daga baya, amma suka ci gaba da tsere Leah saboda addininta na Kirista kamar yadda rahotanni ke cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.