Najeriya

Mutane na kwana a daji saboda ambaliya a Sokoto

Ambaliyar ta lalata gonakin mazauna kauyukan da ke kan iyaka da Sokoto da Nijar
Ambaliyar ta lalata gonakin mazauna kauyukan da ke kan iyaka da Sokoto da Nijar REUTERS/Tife Owolabi

Rahotanni daga jihar Sokoto ta Najeriya na cewa an sake samun ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu kauyuka a kan iyakar Najeriya da Nijar, lamarin da ya tilasta wa jama’ar yankin kwana a dajin Allah bayan sun rasa muhallansu.

Talla

Kauyukan da matsalar ta shafa sun haka da na kananan hukumomin Ilela da Gada da Isa da Sabon Birni da Goronyo.

Ibtila’in ya kuma lalata albarkatun gonan da mazauna yankin suka noma, yayin da suka mika kokon bara zuwa ga hukumomi don agaza musu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren rahoton da wakilinmu daga Sokoto Faruk Muhammad Yabo ya aiko mana kan ambaliyar ruwan.

Ambaliyar ruwa ta sake mamaye kauyukan Sokoto

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.