Najeriya

Zan sanar da matsayina bayan ganawa da PDP- Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC saboda rashin adalci a PDP, in ji mai mataimakinsa kan kafofin yada labarai
Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC saboda rashin adalci a PDP, in ji mai mataimakinsa kan kafofin yada labarai RFIHausa

Tsohon gwamnan jihar Kano ta Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya fitar da wani sakon murya da ke bayyana cewa, zai sanar da matsayinsa bayan ganawa da jam'iyyar PDP. Wannan na zuwa ne a yayin da ake yada rahotannin da ke cewa tuni tsohon gwamnan ya koma jam'iyyar APC.

Talla

Shekarau ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin da uwar jam'iyyar PDP ta dauka na rusa shugabancin jam'iyyar a jihar Kano, matakin da ya ce, ya saba ka'ida.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren muryar Ibrahim Shekarau.

Muryar Ibrahim Shekarau game da PDP

Tsohon gwamnan ya ce, zai fito da kansa don sanar da jama'a game da duk irin matakin da ya dauka nan kusa.

Wannan na zuwa ne bayan kafafen yada labarai sun rawito mataimakinsa na musamman kan kafafen yada labarai, Sule Ya’u Sule na cewa, tuni Shekarau din ya koma APC daga PDP.

A cewar Sule, “ Ina son tabbatar muku cewa, Shekarau ya yanke shawarar ficewa daga PDP zuwa APC sakamakon rashin adalcin da PDP ke nuna masa da magoya bayansa”

Mataimakin nasa ya ce, babu yadda za su ci gaba da zura wa uwar jam’iyyar PDP ido gain yadda take biye wa Rabiu Musa Kwankwaso daga ya koma PDP a ‘yan kwanakin da suka gabata daga APC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.