Najeriya

Magoya bayan Buhari sun saya masa takardar takara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Daniel Leal-Olivas/ Reuters/File Photo

Wata kungiyar magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta saya masa takardar tsayawa takarar zabe akan Naira miliyan 45.

Talla

Kungiyar mai suna 'Nigeria Consolidation Ambassadors Network' (NCAN) ta dauki matakin ne bayan sanarwar da aka fitar a hukumance da ke bayyana ranar da jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da zaben fid da gwani da kuma farashin sayen takardar wato Form a turance.

Tuni aka mika takardar Chek na kudin ga shugaban Jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomole a birnin Abuja a ranar Laraba.

Ana sa ran shugaba Buhari ya samu tikitin wakiltar APC a takarar zaben 2019 mai zuwa, lura da cewa, babu wani fitaccen dan takara da ake ganin zai kalubalance shi wajen neman tikitin a karkashin inuwar Jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.