Najeriya

Yunwa za ta ritsa da mutane dubu 800 a Najeriya

'Yan gudun hijirar Boko Haram na cikin matsalar karancin abinci a Najeriya
'Yan gudun hijirar Boko Haram na cikin matsalar karancin abinci a Najeriya AFP PHOTO: Reinnier Kazé

Kasashen Turai sun gargadi Majalisar Dinkin Duniya cewar, sama da mutane dubu 800 za su fuskanci matsalar yunwa a Najeriya, sakamakon karancin abinci a yankin da ke fama da rikicin Kungiyar Boko Haram. Wannan matsayi ya yi karo da na gwamnatin Najeriya wadda ke cewa ya dace a kawo karshen aikin jinkai domin fuskantar shirin sake gina yankin.

Talla

Wata wasika da Kungiyar Kasashen Turai ta rubuta wa shugabannin aikin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya da ke dauke da sanya hannun kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus, ta zargi Majaisar da gazawa wajen shawo kan bala’in da ake fuskanta wanda ya jefa rayuwar kananan yaran da ke yankin cikin hadari.

Wasikar ta ce, kasashen sun damu matuka kan rahsin daukan matakan gaggawa domin samarwa wadannan mutane sama da 800,000 kayan jinkai, in da suka bukaci wakilan Majalisar da ke Najeriya da su matsa wa gwamnatin kasar wajen ganin ta bada damar kai dauki ga mutanen da suke bukata.

Wasikar ta ce, aikin jinkan ya kasa kaiwa ga mutane 823,000 a Borno, Jihar da tafi shan azabar tashin hankalin.

Kasashen wadanda dukkan su manyan masu bada agaji ne, sun bukaci hadin-kai da kuma aiki tare da gwamnatin Najeriya domin cimma biyan bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI