Najeriya

Sojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 14

Ana kyautata zaton tsagun  Abubakar Shekau ne ya yi garkuwa da fararen hula a Gwoza
Ana kyautata zaton tsagun Abubakar Shekau ne ya yi garkuwa da fararen hula a Gwoza News Ghana

Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta kashe akalla mayakan Boko Haram 14 tare da ceto mutane 21 da kungiyar ta yi garkuwa da su a kauyen Pulka da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.  

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Boko Haram ta yi garkuwa da mutanen jim kadan da kai hari kan ayarin motocin soji.

Mutanen dukkaninsu fararen hula na tafiya ne cikin ayarin motocin, in da suka yi karo da harin kwonton-bauna da mayakan na Boko Haram suka yi musu.

Majiyar tsaro ta shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP cewa, harin ya yi sanadinayr mutuwar wani soja da farar hula guda.

Ana kyautata zaton tsagun Abubakar Shekau da ke rayuwa a yankin dajin Sambisa ne ya kaddamar da harin.

A cikin watan Agustan da ya gabata ne tsagun na Shekau ya ayyana Gwoza a matsayin shalkwatar daularsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI