Najeriya

Masu kada kuri'a a Najeriya za su haura miliyan 84

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Mahmud Yakubu
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Mahmud Yakubu Ventures Africa

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ce adadin masu kada kuri’a a kasar zai haura milyan 84 kafin zabubukan shekara mai zuwa.

Talla

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu, ya ce kafin zabubukan na shekarar badi za su buga wasu katunan zabe sama da milyan 16, kari da milyan 69 da tuni hukumar ta buga, duk da cewa adadin zai iya raguwa zuwa kasa sakamakon aikin tantancewa.

Yakubu ya ce, sun yi wa sabbin masu kada kuri’a sama da miliyan 14 rajista a cikin watanni 16 tun daga watan Afrilun bara zuwa Agustan bana.

Har yanzu ana ci gaba da yi wa mutane rajistan katin zaben a sassa daban daban na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.