Najeriya

Ba ni da kudin sayen takardar takarar zabe- El-Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Daily Post

Gwamnan Jihar Kaduna a Najeriya, Nasir El-Rufa’I ya ce, ba shi da kudin sayen takardar takarar neman tarzace a zabe mai zuwa, yayin da wasu kungiyoyi suka saye masa takardar, wato fom, abin da gwamnan ya ce, ya zo masa da mamaki.

Talla

Gwamnan ya ce, ba don wadandan kungiyoyi da suka saya masa takardar ba, da ya kasance cikin wani hali.

Wadanda suka saya masa fom din sun hada da Kungiyar Dillalan Man Fetir Mai Zaman Kanta a Najeriya (IPMAN) da Kungiyar Masu Motocin Sufuri na Kansu (NARTO) da Kungiyar ‘Yan kasuwar Sheik Mahumud Gumi da kuma Kungiyar ‘Yan Katsina da Daura mazauna jihar Kaduna.

A yayin gabatar da jawabin tarbar jagoran kugiyoyin a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna, El-Rufa’I ya ce, ba shi da Naira miliyan 20 na sayen fom, domin a cewarsa, kudin da yake da shi a asusunsa na banki, ko kusa bai kai adadin kudin sayen fom din ba.

“Asusu daya gare ni a bankin GTB, sai dai na sayar da gidana kafin hada adadin kudin” In ji  gwamna El-Rufa’i.

Wannan na zuwa ne bayan wata kungiya ta saye wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari takardar takarar akan Naira miliyan 45 a yayin da yake halartar wani taro a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.