Najeriya

Mutane da dama sun mutu a gobarar Nasarawa

Jami'an kashe gobara sun kai dauki a wurin da ibtila'in ya auku
Jami'an kashe gobara sun kai dauki a wurin da ibtila'in ya auku rfi hausa

Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wata gobara da ta shi sakamakon fashewar tukunyar iskar gas a wani gidan mai da ke jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya.

Talla

Rahotanni mabanbanta sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 15 ko kuma fiye da haka, yayin da aka kwantar da 40 a asibiti saboda raunin kunar–wuta.

Bayanai na cewa, kimanin motoci 17 da suka hada da tankokin mai guda biyu suka kone kurmus bayan tashin wutar a sashen sayar da iskar gas da ke gidan man Natson da ke Lafiya.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziya ga gwamnatin jihar da al’ummarta kan wannan iblila’in da ya auku a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.