Najeriya

Ana gwabza yaki tsakanin sojoji da Boko Haram a Damasak

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a Borno
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram a Borno STEFAN HEUNIS / AFP

Rahotanni daga Damasak da ke jihar Bornon Najeriya sun ce, yanzu haka dakarun sojin kasar na fafatawa da mayakan Book Haram da suka kai musu hari a sansaninsu da misalin karfe 6 na yammacin yau.

Talla

Mai Magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Janar Texas Chukwu ya ce yanzu haka ana can ana gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin biyu, kuma sojojin Najeriya na samun galaba.

Al'umma na ci gaba da nuna fargaba sakamakon yadda hare-haren Boko Haram ke dada ta'azzara a baya-bayan nan.

Ko a 'yan kwanakin nan, sai dai kungiyar ta kai mummunan farmaki tare da kashe sojojin Najeriya da dama a sansaninsu da ke jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.