Najeriya

Masarautar Kano na gab da fitar da dokar mutuwar aure

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II REUTERS/Joe Penney

Masarautar Kano a Najeriya na aiki tukuru kan wani kudirin doka da zai magance matsalar yawaitar mutuwar aure tare da tilasta wa magidanta daukan cikakkiyar dawainiyar iyalansu.

Talla

Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a gefen wani taro da Asusun Tallafawa al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya a birnin Abuja.

Sarkin wanda Talban Kano ya wakilce sa, ya ce, Masarautar ba za ta lamunce wa maza sakin matansu ba tare da daukan hidimar kulawa da yaransu ba.

Nan kusa za kwamitin da ke aiki kan kudirin dokar zai kammala aikinsa kafin gabatar da shi ga Majalisar Dokokin Jihar don amincewa da shi a matsayin doka.

Kwamitin ya kunshi manyan alkalai da malaman addinin Islama da malaman ilimin zamani na boko.

Ana sa ran dokar za ta taka muhimmiyar rawa wajen rage raragaitar kananan yara a kan titunan jihar matukar gwamnati ta amice da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.