Najeriya

Hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta hana karin girma ga masu katon tumbi

Babban Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya  Ibrahim Idris.
Babban Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris. Daily Post

Hukumar Kula da ‘Yan kasa ta Najeriya ta koka yadda akasarin ‘yan sandan kasar ake samunsu da katon tumbi saboda rashin motsa jiki.

Talla

Daga yanzu Hukumar ta ce duk wani dan sanda mai katon tumbi to kuwa shi da samun Karin girma saidai ya hangi wasu an yi masu.

Wata sanarwa daga Hukumar na cewa bayaga neman kowa ya rage girman tumbinsa dole ne masu bukatan samun Karin girma su yi nasarar cin jarabawa da ake yi masu.

Sanarwar na cewa Shugaban Hukumar  kula da 'yan sanda Musliu Smith ya damu matuka da yadda ake yawaitan sauyawa wasu ‘yan sanda wuraren aiki maimakon a bar mutun ya yi akalla shekaru biyu zuwa uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.