Najeriya

Ministan Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun ta yi murabus

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi takardan ajiye aiki da Ministen Kudi Uwargida Kemi Adeosun ta gabatar masa.

Ministan Kudin kasar Najeriya Kemi Adeosun
Ministan Kudin kasar Najeriya Kemi Adeosun REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban ya godewa tsohuwar Ministan saboda ayyukan da tayi a lokacin da take cikin Gwamnati.

Shugaba Buhari ya amince da karamar Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Uwargida Zainab Ahmed data dare kujeran Ministan Kudin ba tare da bata lokaci ba.

Masu tone-tone ne  suka bankado cewa tsohuwar Ministan kudin Kemi Adeosun ta mallaki takarda shaidan bautan kasa na bogi ne, domin bata yi wa kasa hidima ba bayan kamala karatun jamian wanda kuma laifi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI