Najeriya

Human Rights Watch ta bukaci adalci yayin yiwa 'yan Boko Haram shari'a

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta tabbatar da an yi adalci, yayin gudanar da shari’un wadanda ake zargi da alaka da kungiyar Boko Haram.

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne, bayan kama su a garin Maiduguri.
Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne, bayan kama su a garin Maiduguri. REUTERS/Ahmed Kingimi
Talla

Kiran ya zo ne yayinda wasu ke korafi kan tsarin gudanar da shari’un, da kuma ci gaba da tsare wadanda ake zargi ba tare da gaggauta yanke musu hukunci ba.

A watan Oktoba na shekarar bara, aka soma gudanar da shari’un mutane 1,669 a jihar Niger, bayan shafe tsawon lokaci suna tsare, bisa zargin alakarsu da Boko Haram.

A waccan lokacin dai, an yaba da soma shari’un, sai dai daga bisani, an rika samun korafe-korafe daga bangarori da dama, musamman ma kungiyoyin kare hakkin dan adam, akan yanayin yadda shari’un ke gudana a sirrance, ba tare da baiwa ‘yan jaridu, da sauran al’ummar gari damar sa ido akai ba.

Kan haka ne yasa Kungiyar Human Rights Watch ta yi gargadin cewa, gaza yin adalci yayin gudanar da shari’un ka iya mayarda hannun agogo baya, ta hanyar kara rura wutar rikici ko tayarda kayar baya da mayakan na kungiyar Boko haram suke yi.

Tun bayan soma shari’un zuwa wannan lokaci, rahotanni sun ce an zartas da hukunci kan mutane 113, bisa tabbatar da laifukan alaka da Boko Haram, da suka hada da, zama ‘ya’yan kungiyar, kare hare-haren ta’addanci ko kuma taimakawa kungiyar ta kowace fuska.

Sai dai wasu bayanai daga gwamnatin Najeriya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito, sun nuna cewa, a halin yanzu, an zartas da hukunce-hukunce akan mutane 240 bisa laifukan alaka da Boko Haram, yayinda aka sallami, wasu 1,054 bayan da shari’a ta wanke su, ko kuma aka gaza samar da cikakkun hujjojin tabbatar da laifukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI