Bakonmu a Yau

Farfesa Muhammad Kabir Isa kan matsalar yawaitar yin garkuwa da mutane a Najeriya da wasu kasashen yammacin Afrika

Sauti 03:40
Matsalar sata da yin garkuwa da mutane na ciwa gwamnatocin wasu kasashen yammacin nahiyar Afrika tuwo a kwarya.
Matsalar sata da yin garkuwa da mutane na ciwa gwamnatocin wasu kasashen yammacin nahiyar Afrika tuwo a kwarya. Information Nigeria

Ganin yadda lamarin satar mutane da kuma yin garkuwa da su ke ciwa jami'an tsaron Najeriya tuwo a kwarya da ma na wasu kasashen yammacin nahiyar Afrika musamman makwabtan Najeriyar, masana tsaro na ci gaba da tafka muhawara da kuma tuntubar juna, kan mafita daga wannan matsala.Kan haka ne Garba Aliyu Zaria, ya tattauna da farfesa Muhammad Kabir Isa, na jami'ar ABU Zaria.