Bakonmu a Yau

Najeriya-Italiya

Wallafawa ranar:

Alkalin wata kotu da ke birnin Milan na kasar Italiya, ya yanke hukuncin farko a game da batun bayar da rashawa domin baiwa kamfanonin mai Shell da ENI damar sayen wata katafariyar rijiyar mai a tarayyar Najeriya.Alkalin ya yanke hukuncin daurin shekaru hurhudu a kan mutane biyu Emeka Obi dan Najeriya da kuma wani dan Italiya mai suna Gianluca Di Nardo, bayan da aka tabbatar da cewa su ne manyan dillalan da suka taka rawa wajen kulla ciniki da ya kai dala bilyan daya da milyan 300 a shekara ta 2011.Baya ga daurin a gidan yari, kotun ta kuma kwace milyoyin kudade daga mutanen biyu. Eng Dr Kailani Muhammad tsohon babban jami’i ne a kamfanin mai na NNPC, ga abin da yake cewa dangane da hukuncin.

Kamfanonin mai na Shell da Eni
Kamfanonin mai na Shell da Eni CARL COURT, MARCO BERTORELLO / AFP
Sauran kashi-kashi