Najeriya

INEC da EFCC sun hada gwiwa kan yakar cinikin kuri'u a zaben jihar Osun

Akalla kuri'u miliyan daya ko sama da haka ake sa ran jefawa a zaben gwamnan jihar Osun.
Akalla kuri'u miliyan daya ko sama da haka ake sa ran jefawa a zaben gwamnan jihar Osun. Premium Times/ Ben Ezeamalu

An soma kada kuri'a a zaben kujerar gwamnan jihar Osun, wanda ‘yan takara 48 ke fafatawa a cikinsa inda ake sa ran kada kuri’u akalla miliyan guda ko sama da haka.

Talla

Sai dai kafin soma zaben na yau Asabar, ranar jajiberin zaben, hukumar shirya zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, hadi da hukumar EFCC mai yakar cin hanci da rashawa, sun yi gargadin kamawa da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifin saye ko sayar da kuri’a.

Sakataren yada labaran hukumar INEC Rotimi Oyekanmi ya fitar da wannan sanarwa a Abuja a jiya Juma’a, yayin haramar soma aikin lura da masu kada kuri’a a zaben gwamnan jihar Osun na yau Asabar.

A cewar Oyekanmi, INEC da EFCC sun hada gwiwar aiki tare ne, bayan taron da suka yi a garin Abuja, inda suka amince cewa EFCC za ta rika lura da hada-hadar kudade a bankuna ta hanyar hadin gwiwa da ma’aikatansu, domin zakulo wadanda za su yi yunkurin batar da sawu wajen saye ko sayar da kuri’u.

Wasu daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar ta Osun da ke kan gaba wajen samun karbuwa, sun hada da Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC, Iyiola Omisore na jam'iyyar SDP da kuma Ademola Adeleke ona jam'iyyar PDP.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.