Najeriya

Ambaliyar ruwan bana na gaf da zarta ta shekarar 2012 - NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce yawan wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon ambaliyar ruwan da ta aukawa sassan jihohin kasar 12, ya karu zuwa 101.

Wani yanki na unguwanni a garin Lokoja da ambaliyar ruwa ta mamaye a ranar 17 ga Satumba, 2018.
Wani yanki na unguwanni a garin Lokoja da ambaliyar ruwa ta mamaye a ranar 17 ga Satumba, 2018. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban hukumar ta NEMA, Mustapha Maihaja, ya ce an samu karuwar rasa rayukan ne, duk kuwa da cewa hukumarsa da sauran takwarorinta na kasar a jihohin da Iftila’in ya shafa suna bakin kokarinsu wajen ceto da kuma agazawa wadanda lamarin ya rutsa da su.

Maihaja ya shaidawa manema labarai a garin Abuja cewa, hasashe mafi rinjaye ya nuna cewa yawan ambaliyar da za a fuskanta a bana za ta zarta wadda aka gani a shekarar 2012.

A cewar shugaban hukumar ta NEMA, yayi karin bayanin cewa, a shekarar 2012, tudunta ya kai mitoci 12.84 a ranar 29 ga watan Satumbar shekarar, to amma zuwa ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 2018 da muke ciki, tudun ambaliyar ruwan bana ya kai mitoci 11.21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI