Najeriya

APC ta sauya ranar zaben dan takararta a zaben 2019

APC za ta gudanar da taronta na kasaa  ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa
APC za ta gudanar da taronta na kasaa ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa AFP/Stefan Heunis

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sauya ranar gudanar da zaben fid da gwanin dan takarar shugaban kasa a 2019 kamar yadda Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Yekini Nabena ya fitar a wata sanarwa.

Talla

Yanzu haka za a gudanar da zaben a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba a maimakon 25 ga watan na Satumba da aka shirya gudanarwa da farko.

Ko da yake wannan sauyin bai shafi sauran zabukan fid da gwani ba da suka hada da na gwamnoni da za a yi a ranar 29 ga watan na Satumba da na Sanatoci a ranar 2 ga watan Oktoba, sai na ‘yan majalisar wakilai a ranar 3 ga watan Oktoba.

A ranar 4 ga watan na Oktoba ne za a gudanar da zaben fid da gwani na ‘yan majalisun jihohi, yayin da a ranar 6 ga watan Oktoba jam’iyyar ta APC za ta gudanar da taronta kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.