Najeriya

Osun:PDP da APC za su san makomarsu a ranar Alhamis

Hukumar Zabe a jihar Osun da ke tarayyar Najeriya ta tsayar da ranar Alhamis mai zuwa domin sake gudanar da zabe a wasu yankunan jihar, kafin sanar da wanda ya yi nasara tsakanin Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u dubu 254 da 698 sai kuma Gboyega Oyetola na APC mai kuri’u dubu 254 da 345.

Hukumar Zaben Najeriya ta ce, zaben gwamnan jihar Osun bai kammalu ba bayan soke kuri'u sama da dubu 3
Hukumar Zaben Najeriya ta ce, zaben gwamnan jihar Osun bai kammalu ba bayan soke kuri'u sama da dubu 3 dailytrust
Talla

Wannan dai na nufin cewa tazarar kuri’u 353 ke tsakanin mutanen biyu, yayin da aka soke sakamako a mazabun da ke da kuri’u sama da dubu uku.

Shugaban hukumar zabe a jihar ta Osun Joseph Adeola Fuwape, ya bayyana dalilin sake gudanar da zaben, in da ya ce,

“Bayan nazari a game da sakamakon wannan zabe, mun gano cewa bambancin da ke tsakanin ‘yan takara biyu da ke sahun gaba, duka-duka kuri’u 353 ne, alhali kuwa yawan kuri’un da aka soke sakamakonsu ya kai 3498. Saboda haka, a matsayina na shugaban hukumar zabe na wannan jiha, ba zan iya bayyana wanda ya lashe zaben ba. Ni, Joseph Adeola Fuwape, ina mai sanar da cewa zaben bai kammala ba.”

Rahotanni na cewa, akwai yiwuwar wasu ‘yan adawa su yi hadaka da jam'iyyar PDP don ganin bayan APC a zaben na ranar Alhamis mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI