Najeriya

Dogarin A'isha Buhari ya damfare ta Naira biliyan 2 da rabi

Kafofin yada labaran Najeriya sun rawaito cewa, uwargidan shugaban kasar A’isha Buhari ta bada umarnin cafke babban dogarinta bisa zargin sa da damfarar ta makudaden kudaden da yawansu ya kai Dala biliyan 2.5.

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari
Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari TWITTER/AISHA M. BUHARI
Talla

Uwargida A’isha na zargin Sani Baba-Inna, babban Sufurtandan ‘yan sanda da karbar kudaden na taimako daga hannun ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa a madadinta, sannan ya noke su a aljihunsa.

Tuni A’siha ta bukaci Sufeta Janar na rundunar ‘yan sandan kasar, Ibrahim Idris da ya kama Baba-Inna tare da tilasta masa maido da kudaden bayan ruf da ciki da su.

Yanzu haka ana ci gana da tsare Baba-Inna, yayin da iyalansa da ‘yan uwansa ke cewa, ba su ji duriyarsa ba tun bayan tsare shi a ranar jumm’a.

Sai dai wasu majiyoyin na cewa, wanda ake zargin ya musanta karbar kudaden na taimako daga hannun wani, amma duk da haka ‘yan sanda sun gudanar da bincike a gidansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI