Najeriya

NLC ta kira gagarumin yajin aiki a Najeriya

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta bukaci daukacin mambobinta da sauran kungiyoyin da ke da nasaba da ita da su shiga gagarumin yajin aikin game-gari da ta kira.

Wasu mambobin NLC a Najeriya
Wasu mambobin NLC a Najeriya NLC
Talla

NLC ta ce, ta kira yajin aikin ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza ci gaba da zaman tattaunawa game da amincewa da mafi karancin albashin ma’aikatan kasar.

Shugaban kungiyar Ayuba Waba ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Laraba a birnin Abuja.

A cewar Waba, za a fara yajin aikin ne da tsakar daren ranar 26 ga watan Satumba don ganin gwamnatin ta amince da Naira dubu 50 a matsayin mafi karancin albashi a maimakon Naira dubu 18.

Babbar kungiyar ta kwadago ta bukaci dukkanin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da bankuna da makarantu da giajen man fetir da su shiga yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI