Bakonmu a Yau

Comrade Nasir Kabir mai kula da shirye-shirye na kungiyar kwadagon Najeriya kan yajin aikin gama gari

Sauti 03:20
Wasu 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya.
Wasu 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya. The Guardian Nigeria

Kungiyar Kwadago Najeriya ta sanar da soma yajin aikin gama-gari tun daga wayewar gari yau Alhamis har sai iabinda hali yayi, domin neman gwamnati ta yiwa ma’aikata karin albashi mafi kankanta a kasar.A taron manema labarai a Abuja, gamayyar kungiyar kwadagon ta Najeriya, ta bayyana cewa matakin nasu ya biyo bayan rashin gamsuwa ne da take-taken gwamnati dangane da cika alkawarin da ta dauka.Garba Aliyu Zaria ya nemi karin bayani daga bakin Comrade Nasir Kabir mai kula da shirye-shirye na kungiyar kwadagon ta Najeriya.