Najeriya

'Yan bindiga sun sace masu hakar ma'adanai a Kaduna

An yi garkuwa da masu hakar ma'adanai a Kaduna.
An yi garkuwa da masu hakar ma'adanai a Kaduna. Information Nigeria

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da sace wasu mutane 16 dake aikin hakar ma’adinai a kusa da kauyen Bogoma dake karamar hukumar Birnin Gwari.

Talla

Yakubu Sabo, jami’in yada labaran rundunar dake Jihar Kaduna yace tuni rundunar ta baza jami’an ta domin farautar wadanda suka sace mutanen.

An dai sace ma’aikatan ne a ranar Talata da ta gabata da daddare, a lokacin da suke kan hanyar komawa gida.

Rahotanni sun ce wadanda suka sace mutanen sun tintibi ‘yan uwan su domin biyan kudin fan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.