Najeriya

Oyetola ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Osun

Gboyega Oyetola dan takarar jam'iyya mai mulki APC, da ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Osun.
Gboyega Oyetola dan takarar jam'iyya mai mulki APC, da ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Osun. Premium Times

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayyana Gboyega Oyetola, na jami’yyar APC mai mulki, a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Osun.

Talla

A jiya Alhamis aka kada ragowar kuri’un zaben kujerar gwamnan a wasu rumfunan zabe guda bakwai, wadanda suke kananan hukumomi hudu na jihar ta Osun, saboda dakatar da kada kuri’un, a ranar Asabar din da ta gabata, bisa wasu dalilai da suka hada da na tsaro da kuma sahihanci.

Kananan hukumomin da aka gudanar da cikon zaben kujerar gwamnan sun hada da, Ife ta Arewa, Ife ta Kudu, Kajola da kuma Osogbo.

Yayin sanar da sakamakon, kwamishinan hukumar zaben jihar ta Osun, Farfesa Joseph Fuwape, ya ce Oyetola na jam’iyyar APC, ya lashe zaben gwamnan da kuri’u dubu 255,505, yayinda Adeleke dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP ya samu kuri’u 255,023.

Sai dai tuni jam’iyyar adawa ta PDP, da kuma gamayyar jam’iyyun da suke goyon bayanta suka yi watsi da sakamakon, wanda suka ce babu gaskiya a cikinsa, dan haka za su kalubalanci sakamakon a kotu.

A sakamakon farko da ya bayyana na ranar Asabar a zaben na gwamnan, ya nuna cewa Adeleke na jam’iyyar PDP ke kan gaba da kuri’u 353, bayan samun jimillar adadin kuri’u 254,698, yayinda Oyetola na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 254,345.

Karashen zaben kujerar gwamnan ya dogara ne kan ragowar kuri’u 2,637 da ba’a kada ba, wanda daga karshe APC mai mulki ta samu rinjaye.

Kafin kammala gudanar da zaben gwamnan na Osun dai, dan takarar jam’iyyar adawa ta SDP Iyiola Omisore da ke a matsayi uku, ya zama mutum mai muhimmanci da jam’iyyun APC da PDP ke fafutukar samun goyon bayansa wanda daga karshe APC ta yi nasarar kulla kawance da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.