Isa ga babban shafi
Najeriya

NJC ta bukaci Buhari ya kori wasu alkalan Najeriya

Ginin Hukumar Kula da Ayyukan Alkalan Najeriya, NJC
Ginin Hukumar Kula da Ayyukan Alkalan Najeriya, NJC premiumtimes
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shari’a a Najeriya ta NJC ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gaggauta korar wasu manyan alkalan kasar guda biyu saboda yadda matsalar cin hanci da rashawa ta dabaibaye ayyukansu.

Talla

Mai Magana da yawun hukumar, Soji Oye ya ce bayan taron hukumar gudanarwar da aka yi a karkashin Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, hukumar ta mika sunayen mai sharia Rita Ofili-Ajumogobia da James Agbadu-Fishim a matsayin wadanda suke bukatar ganin an kora.

Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da ke tabbatar da tuhumar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta yi wa alkalan biyu.

A cewar NJC ta dauki matakin ne bayan kammala nazari game da tuhumar ta cin hancin da rashawa da ake yi wa alakalan biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.