Zamfara: Takaddama ta kunno kai a zaben fidda gwani

Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara.
Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara. TheCable

Kwamitin da hedikwatar jam’iyyar APC ya nada domin jagorantar aikin zaben fidda dan takarar gwamnan jihar Zamfara a Najeriya, ya sanar da dakatar zaben a daidai lokacin da ake kan gudanar da shi a jiya Laraba.

Talla

Shugaban kwamitin zaben Injiniya Abba Fari, ya ce ya zama wajibi a dakatar da zaben sakamakon rikicin da ya barke a yankuna da dama na jihar, lokacin da ake tsakiyar gudanar da zaben.

To sai dai gwamnan jihar ta Zamfara mai barin ado Abdul Aziz Yari, ya yi watsi da wannan mataki, inda ya ce za a cigaba da zaben a wannan Alhamis.

Wasu jihohi da jam’iyyar APC ke shirin gudanar da zabubukan fidda ‘yan takararta a zaben kujerun gwmanan a yau Alhamis, sun hada da Adama, Enugu da kuma Kwara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.