Isa ga babban shafi
Najeriya-Birtaniya

Sifeton 'yan sandan Najeriya ya cire kwamishinan Filato

Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris.
Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris. Daily Post

Babban Sifeton ‘Yan sandan Najeriya Ibrahim Idris, ya cire kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato Undie Adie daga mukaminsa, umarnin da ya soma aiki a nan take.

Talla

Yayin da yake sanar da sauyin, kakakin ‘yan sandan jihar Filato, Matthias Tyopev, bai bayyana dalilan daukar matakin ba.

A baya dai cikin watan Yuni da ya gabata, babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya ya taba cire Undie Adie daga mukamin kwamishinan ‘yan sandan Filato, sa’o’i 48 bayan hallaka akalla mutane 200 da wasu ‘yan bindiga suka yi kananan hukumomin Riyom, Jos ta Kudu, da kuma Barkin Ladi.

Sai dai daga bisani, bayan wasu ‘yan kwanaki aka sake maida Adie kan mukaminsa.

A halin yanzu, an bayyana Austin Agbonlahor a matsayin wanda ya maye gurbin tsohon kwamishina Adie.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.