Najeriya

EFCC ta soma shirin tuhumar gwamnan jihar Ekiti mai barin gado

Gwamnan Jihar Ekiti mai barin gado Ayodele Fayose.
Gwamnan Jihar Ekiti mai barin gado Ayodele Fayose. TheCable

Hukumar yakar cin da rashawa ta Najeriya EFCC, ta kafa wata tawaga ta musamman, wadda zata binciki gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose a mako mai kamawa, kan zargin aikta laifin almundahana, kamar yadda jaridar Punch da ake wallafawa a kasar ta rawaito.

Talla

Hukumar Fayose, wanda ya kasance gwamnan jihar Eikiti tun daga ranar 16 ga Oktoba, 2014, zai rasa rigarsa ta kariya daga tuhuma a mako mai zuwa, ranar 16 ga watan Oktoban na 2018, lamarin da zai baiwa EFCC damar bincikarsa, tsarewa da kuma gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.

EFCC na sa ran Fayose zai kai kansa ga hedikwatar ta dake Abuja, domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.

Hukumar yakar cin hanci da rashawar na zargin Fayose da karbar naira biliyan 1 da miliyan 200 daga Sambo Dasuki, tsohon mai baiwa tsohuwar gwamnatin shugaba Jonathan shawara kan sha’anin tsaro.

A waccan lokacin dai an rawaito cewa Fayose ya yi amfani da kudin ne, wajen yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar Ekiti, wanda ya lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.