Najeriya

Yara 833 sun janye daga yakin da ake yi da Boko Haram

Sojojin Najeriya na samun taimakon mayakan sa kai a yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya na samun taimakon mayakan sa kai a yaki da Boko Haram STEFAN HEUNIS / AFP

Kungiyar 'Yan Kato da Gora a Najeriya da ke taimaka wa dakarun kasar yaki da Kungiyar Boko Haram ta mika matasa 833 da ke karkashinta da kuma shekarunsu bai haura 18 ba ga gwamnatin jihar Borno.

Talla

Wannan ya biyo bayan alkawarin da kungiyar ta dauka a bara na daina amfani da yaran da ba su wuce shekaru 18 ba.

Mataimakin Shugaban Hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Pernille Ironside ya ce, matakin na fitar da wadannan yara daga cikin kungiyar ya tabbatar da aiwatar da dokokin duniya na kare hakkokin yara.

Tun bayan kulla yarjejeniyar da kungiyar ta yi a watan Satumbar bara, matasa 1,469 da suka kunshi maza 1,175 da 'yan mata 294, aka gano cewar suna cikin kungiyar a birnin Maiduguri.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 27,000 a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.