Najeriya

Majalisar Kano na bincike kan zargin Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Daily Post

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta Najeriya ta kafa kwamitin mutun bakwai don gudanar da bincike game da sahihancin faye-fayen bidiyon da ke nuna Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje na karbar bandir-bandir na Dalar Amurka a matsayin cin hanci daga wani dan kwangila.

Talla

Kafa kwamitin na zuwa bayan dan Majalisar da ke wakiltan mazabar Warawa, Labara Madari ya bukaci gudanar da bincike kan bidiyon wanda gwamnatin jihar ta musanta.

Kwamitin binciken na karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a Majalisar, Baffa Babba Dan-Agundi.

Dan Agundi ya ce, matukar suka tabbatar da sahihancin bidiyon, za su sanar da Majalisar don daukan mataki na gaba, amma muddin suka gano akasin haka, to za su umarci gwamnatin Kano da ta dauki matakin shari’a kan Jaridar Daily Nigerian da mawallafinta.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren rahoto kan kafa kwamitin binciken.

Rahoto kan kwamitin binciken Ganduje

A cewar Dan Agundi, yanzu haka sun dakatar da gwamnatin Kano daga shigar da maganar a kotu har sai an kammala gudanar da bincike.

Kakakin Majalisar, Kabiru Rurum ya bukaci kwamitin da ya gabatar da sakamakon bincikensa cikin wata guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.