Isa ga babban shafi
Amurka

Ba ma goyon bayan wani dan takara a Najeriya- Amurka

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari zai fafata da Atiku Abubakar a zaben 2019.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fafata da Atiku Abubakar a zaben 2019. Sahara Reporters
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Amurka ta ce, babu wani dan takara da take mara wa baya a zaben Najeriya na shekarar 2019, in da za a fafata tsakanin shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Talla

Jami’in da ke kula da harkokin siyasa a ofishin Jakadancin Amurka, Phillip Franz ya bayyana haka a yayin zantawa da manema labarai a jihar Katsina jim kadan da kammala ganawa da mahukuntan jihar.

Franz ya ce, abin da Amurka ke goyon baya shi ne tsare-tsaren gudanar da zaben, in da ya ce, suna matukar mutunta ‘yancin Najeriya.

A cewar jami’in, Amurka na goyon bayan gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali, yayin da ya ce, a shirye suke su bada dukkanin gudunmawa don gaanin zaben ya gudana cikin lumana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.